Gwamnatin Kano Ta dawo da sunan makarantar Yusuf Maitama Sule zuwa North West

FB IMG 1732908820957

Cikin wata sanarwa da kwamishinan ma’aikatar ilimi mai zurfi ta jihar Kano Dr. Yusuf Kofar Mata ya wallafa a shafinsa na facebook, ya ce, a zaman majalisar zartarwar jihar kano na 21 da ya gudana karkashin jagorancin gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, majalisar ta amince da maidawa jami’ar sunanta na asali wato NORHTWEST UNIVERSITY, Kano.

Alfijr Labarai ta rawaito majalisar zartarwar ta amince a sanya sunan na Yusuf Maitama Sule a sabuwar kwalejin ilimi ta karamar hukumar Ghari domin girmamawa ga mai sunan.

Kofar Mata ya kuma bayyana cewa tuni aka bayar da umarnin tura wadannan dokoki zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano domin zamar da su doka, ciki har da gyaran dokar shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga furofesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *