Shugaban Faransa, Macron ya yaba tare da jinjinawa shugaban Najeriya yayin wata ganawa.

FB IMG 1732886085639

Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ya yabawa Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, bisa amfani da irin kuzari da jajircewar da ya nuna a Legas wajen inganta ci gaban Najeriya.

Alfijir Labarai ta rawaito Macron ya yi wannan jawabi a ranar Alhamis yayin wani taron manema labarai da suka gudanar tare da Tinubu a Faransa, inda shugaban Najeriya ke ziyara tun daga ranar Laraba.

A yayin tattaunawar kan karfafa dangantaka tsakanin Faransa da Najeriya, Macron ya jinjinawa shugabancin Tinubu, musamman kan jajircewarsa wajen inganta tsaro a yankin ECOWAS.

Shugaban Faransa ya kuma jaddada yadda Tinubu ke karfafa kwarin gwiwa ga masu zuba jari daga Faransa da sauran kasashen duniya, wanda ke sanya Najeriya zama wurin da ya dace don zuba jari.

“Ina son taya ka murna kan shugabancinka da kuma burin da kake da shi na yin aiki tare da mu. Ina godiya gare ka, Shugaba, bisa wannan ziyarar kasashen waje. Ina godiya bisa kuzari da kwazonka.

“Bayan ka sauya jihar Legas, yanzu kana amfani da wannan kuzarin don sauya kasarka zuwa mafi kyau.

“Kuzarin da muka gani daga ministocin ka, masu zuba jari, da al’ummomin kasuwanci ya gamsar da mu kwarai a Faransa da kuma daukacin duniya don zuba jari a kasarka, sannan mu sanya Najeriya a matsayin babban abokin huldar yanzu da nan gaba,” inji Macron.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *