Gwamnatin Kano Ta Ja hankalin Malaman Jami’o’i Da Kwalejoji Wajen Wayar Da Kan Al’umma Domin Kawo Sauye Sauye A jihar

PXL 20251018 113442427

Gwamnatin Jihar Kano Ta Ja hankalin malaman gaba da Sakandare da ke fadin jihar domin amfani da Iliminsu da gogewarsu wajen taimakawa gwamnati kan wayar da kan al’umma, domin kawo sauye sauye a bangaren tattalin arziki da zamantakewa da tsaro a fadin jihar.

Kwamishinan yaɗa labarai da al’amuran cikin gida Camarde Ibrahim Abdullahi Waiya ne yayi wannan kiran yayin kaddamar da wata kungiya da malaman jami’o’i da kwalejoji suka kafa a jihar Kano mai suna (Forum Of Progress Academics) a yau asabar 18th October 2025

Waiya ya kara da cewar jami’o’i da kwalejoji ba wajene na bada mukala da lakcoci tare da yi wa ɗalibai jarraba! A a wajene na  ilmi wanda Allah ya hore masu ilmi da za suyi amfani da shi wajen warware wasu matsaloli da ake fuskanta a jihar Kano da kasa baki daya.

Lokaci yayi da za a ce wadannan shehunan malamai da Allah ya albarci wannan jihar da su zasu fito su daina boye kansu domin taimakowa gwamnati wajen magance dukkan wata matsala da ta shafi al’umma a jihar. In ji Waiya.

Ya kara da cewar a baya munyi sakaci wajen barin rayuwarmu a hannun jahilar wadanda basu da wani cikakken ilmi yau saboda siyasa su suke haskawa al’umma fitilar rayuwarsu, duk tarin masu ilimin da muke da su da masana amma wannan sakacin ja da baya yasa mun fada hannun yan sari, su suke da damar magana da gwamna ko minista uwa uba shugaban kasa ma, duk wannan yana faruwa ne a rashin shigowar masu ilmi cikin siyasa da shugabanci.

Ina jan hankalinku da ku fito a dama daku a cikin siyasa, duk da wasu na bata siyasar da cewar mugun wasa ne, amma ni a wajena ba haka bane, tunaninka kamanninka, kuma ko wane tsuntsu kukan gidansu yake yi.

A ƙarshe Kwamishinan ya nemi a manta da wannan tsohuwar al’adar da zaka ga a jami’o’inmu da kwalejojinmu suna yi na lalubo wata gagarumar matsala sannan a zauna a tattauna akan yadda za’a magance wannan matsalar amma fa duk a cikin makarantar! Da an kammala sai a debi takardun a kaisu Library a ajiye su shikenan!

Ya kamata nan gaba idan za’ayi irin wannan ya kasance an fito da matsalar a kuma nemi masu irin wannan matsala a tattauna dasu a cikin al’umma kuma kaga wannan zai taimakawa gwamnati wajen warware matsaloli da dama.

Muna kira gareku da cewar duk wani mai yiwuwa wajen taimakon da gwamnatin jihar Kano zata bayar domin kawo muku tallafi domin dabbaka wannan manufa insha Allah zamu yi, nisanku da gwamna Alh Abba Kabir Yusuf ya zo kusa.

Allah ya albarkaci jihar Kano da Najeriya baki daya ameen.

Taron dai an gabatar da shine a dakin taro na Mambayya dake gwammaja a birnin Kano, wanda ya sami masu gabatar da makaloli Kamar Farfesa Ibrahim Barde, Farfesa Ahmed Ibrahim, Farfesa Ahmad Usman, Farfesa Bello Ibrahim, Dr Abubakar Isa Ibrahim, Dr Ali Umar

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *