Rundunar Yan Sandan Kano Sun Cafke Wasu Mutane 5, Jami’an Bogi A Jihar

1002315021

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwar da Kakakin rundinar CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya sanar a shafinsa na Facebook, ya ce, an kama mutanen  da kayyaki ciki har da katin aiki ‘yan sanda na bogi , da ankwa ,da  kudi na CFA 2,500, da kudin Najeriya harma da motarsu kirar Fijo 406 mai launin shuɗi wadda ke da lambar rijista NSR-189-BD.

Wadanda aka kama sun hadar da:
Aliyu Abbas, mai shekara 35, Sani Iliyasu, mai shekara 47, Ashiru Sule, mai shekara 41, Abubakar Yahaya, mai shekara 45 sai Adamu Kalilu, mai shekara 45.

A yayin bincike, wadanda ake zargin sun amince da laifinsu, inda suka bayyana cewa suna amfani da katin aikin ‘yan sanda na bogi don karɓar cin hanci da zaluntar jama’a a jihohin Kano, Katsina tare da jihar Kaduna.

Rundinar ta ce za a gurfanar da su gaban kotu bayan kammala bincike, domin girbar abinda suka shuka! Allah ya cigaba da kare mana jiharmu da kasar mu baki daya ameen.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *