Gwamnatin Kano Ta Samar Da Hanyoyin Da Za a Bi Sakamakon Fara Aikin Gadar Tal’udu

FB IMG 1713485414232

A kokarin gwamnatin jihar Kano na rage cunkoson ababan hawa a cikin birnin Kano sakamakon fara aikin gadar sama, yanzu haka an kammala kananun tituna kimanin guda 5 wanda masu ababen hawa zasu dinga amfani da su har zuwa lokacin da za’a kammala aikin wannan gadar ƙasa (Underpass tare da Gadar Sama, Flyover) a shataletalen Tal’udu.

Alfijir Labarai ta ruwaito Engr Marwan Ahmed Aminu, MNSE kwamishinan hukumar ayyuka da gidaje ya bayyana cewar, domin samun damar yin aiki cikin nustuwa da kwanciyar hankali, za a rufe sassan titin Muhammad Abdullahi Wase daga ranar Alhamis 18/4/2024.

A bisa buƙatar sauƙaƙa zirga-zirga ga masu ababen hawa, ma’aikatar ayyuka da gidaje ta jihar Kano ta samu nasarar samarwa tare da gyaran hanyoyin da za a yi amfani da su domin kyaucewa wurin da aka rufe.

An samar da titunan yanke ta cikin unguwanni kamar haka:

1- Titin Muhammad Abdullahi Wase (Rahama Street zuwa titin Aminu Kano (W.A.A RANO Filling Station).

2- Titin Aminu Kano zuwa titin Muhammad Abdullahi Wase (Kusa da makarantar Adamu na Ma’aji).

3- Titin Muhammad Abdullahi Wase (Layin Nufawa zuwa titin Aminu Kano, layin Mai Tangaran).

4- Titin Aminu Kano (Shaho Street zuwa titin Muhammad Abdullahi Wase).

KNSG FLYOVER TAL"UDU
KNSG
FB IMG 1713485685419
KNSG
FB IMG 1713485682711
KNSG
FB IMG 1713485680103
KNSG

Haka kuma ana shawartar masu ababen hawa da su nisanci wurin da ake gudanar da wannan katafaren aiki idan ba ya zama dole ba, domin samun zirga-zirga cikin nutsuwa kuma rage cunkoso.

Gwamnatin jihar Kano tana ƙara neman goyon baya tare da haɗin kan jama’a domin samun nasarar wannan aiki da zai inganta rayuwarmu, bunƙasa kasuwanci tare da kyautata zirga-zirga cikin yanayi mai sauƙi.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *