Za a cigaba da zikirin sabuwar Shekara kamar yadda aka Saba, wanda marigayi mai Martaba Sarkin Kano Alh Ado Bayero ya assasa a gidan Sarki na cikin gari.
Alfijir labarai ta ruwaito Mai Martaba Sarkin Kano Alh Aminu Ado Bayero yayin jawabinsa a wajen taron Zikirin Juma’a na Karshen shekara a jiya Juma’a yace, an dabbaka wannan zikiri na karshen shekara a gidan Nassarawa insha Allahu kuma duk shekara za a dinga gudanar dashi domin godiya ga Allah da ya bamu ikon ganin Karshen shekara lafiya.
Ya kara da cewar za a cigaba da zikirin sabuwar Shekara kamar yadda aka Saba, wanda marigayi mai Martaba Sarkin Kano Alh Ado Bayero ya assasa a gidan Sarki na cikin gari.
Kuma insha Allahu wannan shekara da zamu shiga za a gudanar bisa Jagorancin Mai Martaba Sarki Kamar yadda aka Saba insha Allahu.
Allah Ubangiji ya amsa dukkan Addu’oi da akayi. Allah ya karbi ambato da kirarin da akayi Masa.
Ameen summa Ameen.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj