Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayar da naira biliyan 17 ga gwamnatin jihar Bauchi domin bunƙasa sha’anin aikin hakar man fetur da iskar gas tare kuma da gina makarantar nazarin harkokin albarkatun mai a yankin Kolmani dake garin Alkaleri a yankin jihar Bauchi da Gombe.
Ƙaramin ministan albarkatun man fetur na kasa Mr. Heineken Lokpobiri ne ya tabbatar da hakan jiya Asabar 17 ga wata a garin Alkaleri dake jihar Bauchi yayin bikin kaddamar da makarantar.
Ƙaramin ministan a ma’aikatar man fetur na tarayyar Najeriya ya ce bisa la’akari da muhimmancin makamashi ga sha’anin ci gaban tattalin arzikin kasa, shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da fitar da naira biliyan 17 domin tabbatuwar sabuwar makarantar nazarin albarkatun mai dake Alkaleri a jihar Bauchi, wadda za ta rinka bayar da horo ga dalibai da suka fito daga kowanne sashe na ƙasa.
A jawabinsa, gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad ya ce, an fara tunanin samar da makarnatar ce a Alkaleri tun a shekara ta 2021 sakamakon gano man fetur da iskar gas mai yawan gaske a yankin Kolmani dake yankin Alkaleri da kuma jihar Gombe.
Gwamnan jihar na Bauchi ya jaddada ƙudurin gwamnatin jihar wajen bayar da kulawa sosai ta fuskar kyautata sha’anin ilimin kimiyya da fasaha da sauran fannoni domin samar da damammakin aikin yi daban daban ga matasa.
“Wannan ne ma ya ba mu kwarin gwiwar ganin cewa, makarantar nazarin harkokin man fetur da iskar gas ta Bauchi ya zama tabbatacce domin amfanuwar jihar da ma daukacin jahohin dake arewa maso gabashi da ma Najeriya baki daya.”
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD