Gwamnatin Najeriya ta dakatar da kamfanin jirgin saman Max Air

FB IMG 1738156072389

Daga Aisha Salisu Ishaq

Gwamnatin Najeriya ta hannun Hukumar kula da sufurin jragen sama ta ƙasar (NCAA) ta sanar da dakatar da ayyukan kamfanin jirgin sama na Max Air, bayan jirgin kamfanin ya yi hatsari a daren jiya Talata a jihar Kano.

Daraktan hulɗa da jama’a da kare haƙƙin abokan hulɗa na hukumar, Michael Achimugu – wanda ya fitar da sanarwar – ya ce dakatarwar za ta soma aiki ne a daren 31 ga watan Janairun 2025, domin bai wa hukumomin kamfanin damar tattance ayyukanta a cikin gida da ya haɗa da bincike kan kamfanin, ma’aikatansa, tsarin aikinsa da jiragensa, da kuma tattalin arziƙin kamfanin.

Achimugu yace tuni hukumar tabbatar da kariya (NSIB) ta ƙaddamar da bincike kan musabbabin haɗarin na baya-bayan nan.

Jirgin Max Air samfurin B734 mai lambar rijista 5N-MBD, ya yi haɗari ne a yayin sauka a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano da ke Kano bayan tayarsa ta fashe a jiya Talata.

Duk da dai fasinjoji 53 da ke cikin jirgin sun fita lafiya, hukumar kula da filayen jiragen sama ta ƙasar (FAAN) ta rufe filin jirgin na wucin-gadi kafin buɗe shi a safiyar ranar Laraba.

Wannan ne karo na uku da ake samun haɗarin jirgin na Max Air a cikin wata uku.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *