Daga Aminu Bala Madobi
Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire JAMB ta ce ba za ta gudanar da jarabawar shiga jami’a ba, a Jami’ar jihar Kwara (KWASU) da wasu jami’o’i 7.
Mai magana da yawun hukumar ta JAMB, Dr Fabian Benjamin ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.
A cewarsa, an dauki matakin ne na dakatar da karatun digiri na biyu (LL.B) wanda majalisar gudanarwar ilimin shari’a (CLE) ta yi na shekarar karatun 2025/2026 a jami’o’in.
Jami’oin da abin ya shafa sun hadar da
1. Jami’ar Kwara dake Malete.
2. Jami’ar Bingham, Karu, Jihar Nasarawa
3. Jami’ar Redeemers, Ede, Jihar Osun
4. Jami’ar Western Delta, Oghara, Jihar Delta
5. Jami’ar Jihar Taraba Dake Jalingo
6. Jami’ar Arthur Jarvis, Akpabuyo, Jihar Kuros Riba
7. Jami’ar Tarai ta Alex Ekwueme Federal University, Dake Ndufu-Alike, Jihar Ebonyi
8. Makarantar Koyon aikin Yan sanda Dake Wudil, Jihar Kano.
Ya ce dakatar da shirin a makarantar horar da ‘yan sanda ta Najeriya da ke Wudil a jihar Kano, zai dauki tsawon zaman karatu biyu: musamman na 2025/2026 da 2026/2027.
A halin da ake ciki, tun da farko Hukumar JAMB ta sanar da rajistar, da kuma ranakun jarrabawar 2025 na shekarar karatun 2025/2026
Ishaq Oloyede, magatakarda kuma Shugaban hukumar ta JAMB wanda ya bayyana hakan a wata ganawa da shugabannin kafafen yada labarai a Legas, ya bayyana cewa za a fara jarabawar UTME ta 2025 ne a ranar 8 ga Maris, 2025, tare da jarrabawar izinin shiga jami’oi a ranar 23 ga Fabrairu, 2025.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ