Gwamnatin Najeriya ta dauko malamai 313 da ƙarin wasu fastoci domin yiwa Najeriya addu’a har tsawon mako guda a Abuja
Uwargidan Shugaban ƙasa Oluremi Tinubu da NSA, Nuhu Ribadu za su jagoranci wani taron yiwa ƙasa addu’a na tsawon sati guda domin neman Allah ya kawo wa Najeriya sauƙi daga dukkan abunda ke damunta.
Alfijir labarai ta ruwaito Daraktan kula da yiwa Najeriya addu’a Chief Segun Balogun Afolorunikan, (NPF) ya ce an dauko malamai 313 da za su zauna a masallacin Abuja suyi ta sauke Al-Qur’ani har tsawon mako guda wanda ana sa ran za su yi sauka sau 2,191 da nufin Allah ya dafawa Najeriya ya kawo mata sauki.
Su kuma Kiristoci za su hadu a babban cocin Abuja domin yin addu’a tsawon kwana bakwai, kuma ya ce an tuntubi Sarkin Musulmi da Shugaban CAN wajen tattaro malamai da alarammomi da fastocin da za su yi addu’ar “muna da yakinin shiga shekarar 2025 da kafar dama” inji Balogun
Allah duk wanda yake da hannu a dagulewar Najeriya da sauran ta’addanci Allah ya kawo mana karshensa
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj