Gwamnatin Najeriya ta ja kunnen kamfanin Facebook

Alfijr

Alfijr ta rawaito Lai Mohammed ministan watsa labarai da al’adu na Nijeriya ya buƙaci shafin Facebook da sauran shafukan sada zumunta da su daina barin ƴan ƙungiyar IPOB da ke fafutikar kafa ƙasar Biafra su rinƙa amfani da shafin wurin neman tayar da zaune tsaye ko kuma haɗa rikicin ƙabilanci.

Lai Mohammed ya bayyana cewa tun da gwamnatin tarayya ta ayyana IPOB a matsayin ƴan ta’adda, Facebook ba shi da hurumin ba yan IPOB damar bayyana ra’ayinsu.

Ya bayyana haka ne a Abuja a ranar Talata 17th May 2022, bayan wata tattaunawa da ya yi tare da wakilan kamfanin Facebook.

Alfijr

Ministan Ya ce a yanzu gwamnatin Najeriya za ta ci gaba da sa ido kan Facebok da sauran shafukan sada zumunta a ƴan kwanakin nan domin tabbatar da cewa sun bi ƙa’idoji, duk da cewar an dade ana ta ƙorafi ga Facebook kan ayyukan ƴan IPOB, amma kamfanin bai yi komai ba da zai dakatar da su yin ayyukan nasu.

Slide Up
x