Da Ɗumi Ɗuminsa! Kwamishinan Yan Sandan Kano Ya Ce Ba Bomb Ne Ya Tashi Ba Fashewar Tukunyar Gas ne

Alfijr ta rawaito Bam ya tashi a Aba Road da ke Unguwar Sabon Gari a birnin Kano.

Wasu da abin ya faru a gabansu sun tabbatar wa da alfijr faruwar lamarin, sun ce lamarin ya rutsa da mutane da dama ciki har da yara ƴan makaranta.

Wata majiya ta tabbatar mana da cewar tukunyar gas ne yayi wannan sanadin.

Shima a nasa bangaren Kwamishinan yan sandan Kano ya tabbatar da cewar fashewar tukunyar Gas ne.

Slide Up
x