Gwamnatin Najeriya Za Ta Kawo Ƙarshen Shigo Da Kayan Abinci Kasar – Minista

Kayan Abinci

Nijeriya na shirin rage dogaro da shigo da kayan abinci, acewar ministan kudi da tattalin arziki, Wale Edun wanda ya bayyana matakan da ake dauka na bunkasa samar da abubuwan da ake nomawa a cikin gida da kara yawan abincin da ake samarwa.

Alfijir labarai ta rawaito Edun, wanda ya yi bayani a yayin taron manema labarai a Abuja ranar Alhamis a ci gaba da bikin tunawa da ranar samun ‘yancin kan Nijeriya karo na 64, ya bayyana cewa dole ne a kawo karshen shigo da abinci, inda ya bayyana hakan a matsayin matakin Gwamnati na farfado da tattalin arziki ba.

“Bai kamata mu dinga shigo da abinci ba”, inji Edun, inda yayi bayanin cewa nan gaba Nijeriya zata wadatar da kanta.

Acewar sa, Gwamnati ta himmatu wajen tallafawa kananan manoma da kayan noma kamar iri da takin zamani a karkashin shirye shiryen gwamnati na bunkasa noma.

Tallafin zai mayar da hankali wajen bunkasa noman rani da kuma rage bukatar shigo da kayan abinci na matsakaicin zango da kuma bunkasa samar da abinci na zango mai tsayi.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *