Gwamnatin Nigeria ta wajabta gwajin miyagun kwayoyi kafin daukar ma’aikata

FB IMG 1763928899556

Gwamnatin Tarayya ta wajabta yin gwajin ta’ammali da miyagun kwayoyi ga masu neman aikin gwamnati.

Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya ya umarci manyan sakatarori da shugabannin ma’aikatu da hukumomin gwamnati su sanya gwajin miyagun ƙwayoyi a matsayin muhimmin sharadi wajen ɗaukar sabbin ma’aikata.

Sanarwa da Daraktan Hulɗa da Jama’a na Ofishin Segun Imohiosen, ya fitar a ranar Litinin, ta umarci ma’aikatu, hukumomi da sassan gwamnati su yi aiki tare da Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) wajen gudanar da gwaje-gwajen bisa ka’idoji da tsare-tsare da aka kafa.

Sanarwar ta ce: “Gwamnatin Tarayya ta amince da shigar da gwajin miyagun ƙwayoyi kafin daukar ma’aikata aikin gwamnati, a matsayin wani bangare na ƙoƙarin dakile yawaitar shan miyagun ƙwayoyi da illolinsa ga ci gaban ƙasa da tsaro.”

A cewarsa, umarnin ya yi daidai da kudirin wannan gwamnati na yaki da matsalar shan miyagun ƙwayoyi da kuma kare ma’aikatan gwamnati daga dabi’u marasa kyau.

Ya ce wannan manufofi sun samo asali ne daga damuwar da gwamnati ke da ita kan yawaitar shan miyagun ƙwayoyi musamman a tsakanin matasa.

“Umarnin da ya shafi shigar da gwajin miyagun ƙwayoyi kafin daukar ma’aikata ya samo asali ne daga damuwar Gwamnatin Tarayya kan yawaitar shan miyagun ƙwayoyi, musamman a tsakanin matasa, wanda ke da mummunan tasiri ga lafiyar jama’a, ci gaban tattalin arziki, ingancin aiki da tsaron ƙasa.”

Wannan mataki na daga cikin jerin manufofin yaki da miyagun ƙwayoyi da aka gabatar a shekarar 2025.

A watan Nuwamba, Hukumar Kwastam ta Najeriya ta sanya gwajin miyagun ƙwayoyi ga dukkan sabbin ma’aikata da jami’an da ke aiki domin ƙara ladabi da tsaron iyakoki.

Haka kuma, a watan Yuli, an amince da gwajin miyagun ƙwayoyi a dukkan jami’o’i, alamar ƙoƙarin ƙasa baki ɗaya wajen magance matsalar shan miyagun ƙwayoyi.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *