Alfijr ta rawaito wasu shaidun gani da ido sun tabbatar da Kobewar wasu gidaje sakamakon harbin wata mota da jami’an Hukumar kwatsam masu kula da iyakokin Jigawa da Jamhuriyyar Nijar suka yiwa wata mota kirar tanka mai dauke da gas, wanda hakan ya yi sanadin konewar gidaje da shagunan al’umma a karamar hukumar Babura dake jihar jigawa.
Alfijr Labarai
Amma a wata sanarwa da hukumar NSCDC ta jihar Jigawa ta fitar a ya litinin 13 ga Satumba, 2022 tace.
A ranar Litinin, 12 ga Satumba, 2022, da misalin karfe 21:00 na safe, wata mota (Iveco van) da ke dauke da bututun iskar gas ta fashe a karamar hukumar Babura.
Gidaje da shaguna da dama sun kone, wasu kumasun Sami raunuka da yawa amma ba a sami rahoton mutuwa ba a har zuwa lokacin da ake hada wannan rahoton
Alfijr Labarai
Yanzu haka dai wadanda suka jikkata na samun kulawar likitoci a babban asibitin Babura.
Jami’an kashe gobara da suka fito daga karamar hukumar Hadejia da jami’an tsaro da sauran al’umma, an shawo kan wutar da ta tashi.
Hukumar NSCDC sun ce za su fito da musabbabin afkuwar lamarin