Hasken Rayuwa: Ma’aikatar Ilimin Ta Jihar Kano Ta Sanar Da Ranar Rufe Makarantu A Jihar

IMG 060826 031225 1764738526003

Ma’aikatar Ilimin Jihar Kano ta bayyana cewa makarantun firamare da sakandare na gwamnati da masu zaman kansu, na kwana da na jeka ka dawo za su fara hutun zangon farko a ranar Asabar 13 ga Disamba, 2025.

A cikin sanarwar da darktan wayar da Kan jama’a na ma’aikatar Musbahu Aminu Yakasai ta fitar, an bukaci iyayen da ya’yansu suke makarantun kwana da su je su dauko ya’yansu daga ranar Juma’a 12 ga Disamba, 2025.

An tsara cewa ɗaliban makarantun kwana za su koma makarantu a ranar Lahadi 18 ga Janairu, 2026, yayin da ɗaliban makarantun jeka ka dawo za su koma Litinin 19 ga Janairu, 2026.

Zangon karatu na biyu zai fara ne a ranar Lahadi 18 ga Janairu, 2026 kuma ya ƙare a ranar Asabar 18 ga Afrilu, 2026. Zangon uku kuwa zai fara ranar Lahadi 3 ga Mayu, 2026, ya kuma ƙare ranar Asabar 1 ga Agusta, 2026.

Sanarwar ta ce “Jadawalin ya kuma nuna cewa ɗalibai za su yi kwana goma na azumin Ramadan a cikin makarantu kafin a tafi hutun Sallah, wanda zai fara daga Lahadi 1 ga Maris, 2026 zuwa Asabar 21 ga Maris, 2026.

Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Gwani Dr. Ali Haruna Abubakar Makoda, ya yi kira ga iyaye da masu kula da ɗalibai su bi jadawalin da aka amince da shi yadda ya kamata. Ya kuma gode wa al’ummar jihar bisa haɗin kai da goyon bayan da suke bai wa ma’aikatar, tare da yi wa ɗalibai fatan hutu mai albarka da lafiya.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *