Hon Sha’aban Sharada Ya Ƙaddamar Da Takararsa Ta Gwamna A Jam’iyyar ADP

Alfijr ta rawaito ta rawaito Ɗan takarar gwamnan Kano a jam’iyyar ADP, Hon Sha’aban Ibrahim Sharada, ya ƙaddamar da takararsa a hukumance

Alfijr Labarai

Sha’aban ya ƙaddamar da takarar tasa ne a yranar Asabar a cibiyar horas da matasa sana’o’i ta Sani Abacha Youth Center da ke kan titin zuwa Madobi a jihar Kano.

A jawabinsa yayin ƙaddamar da takarar, Malam Sha’aban Ibrahim Sharada, ya ce, ya shiga jam’iyyar ta ADP ne kasancewarta jam’iyyar ba ta yi wa kowa laifi ba.

Haka kuma ya ƙara da cewa, matuƙar ya kafa gwamnati a jihar Kano zai tabbatar da cewa, dukkan asibitocin jihar Kano sun samu wadatattu kuma ingantattun kayayyakin aikin lafiya a duk fadin kananan hukumomi 44.

Alfijr Labarai

Ya ƙara da cewa yanzu haka a jihar Kano babu wata jam’iyya da take samun magoya baya a jihar Kano kamar jam’iyyar ta ADP


Sha’aban ya ƙara da cewa “Idan na kafa gwamnati zan tabbatar da cewa ƙananan hukumomi sun samu cikakken ƴancin cin gashin kai sabanin yadda wasu gwamnatocin suka shake musu wuya. 

Sha aban ya yi kira  ga matasa kan su fito su tabbatar sun kasa masa kuri a don a sami gwamnatin matasa, kuma yace baya nema a wajen kowa sai Allah 

A nasa jawabin, shugaban jamiyyar ta ADP na jihar Kano ya ce, daga shigar Sha’aban jam’iyyar zuwa yau, fiye da mutane dubu Sittin ne suka shiga jam’iyyar kuma duk sun ya ƙi katinta


Haka kuma ya ƙara da cewa, yanzu haka katin zama mamba a jam’iyyar ya ƙare sakamakon tururuwar da mutane ke yi a cikinta.

Alfijr Labara

Haka zalika yayin taron, jam’iyyar ta ADPta karɓi kimanin mutane dubu Sittin daga jam’iyyun APC da PRP kuma jam’iyyar NNPP.

mambobin jam’iyyar waɗanda suka sauya sheƙa daga zuwa ADP ƙarƙashin jagorancin Alhaji Bashir Yahaya Ƙaraye
Yayin taron, fitaccen ɗan siyarsar nan na jam’iyyar APC Alhaji Zubairu Usman Dambatta, ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar APC zuwa ADP.

Yayin jawabin ficewar tasa, Alhaji Zubairu, ya bayyana ɓacin ransa bisa yadda ya ce, jam’iyyar da ya yi wa bara’ar watau APC ta lalata sassan jihar Kano da dama musamman wajen cunkushe kasuwanni da makarantu da gine-gine tare da yanka filaye a maƙabartu.

Shi ma Alhaji Balarabe tsohon mamba a jam’iyyar PRP, ya bayyana sauya sheƙar ɗaukacin mambobin jam’iyyar na ƙananan hukumomin arba’in da huɗu zuwa jam’iyyar ta ADP.

Taron ƙaddamar da takarar ta Sha’aban Sharada, ta samu hartar shugabannin jam’iyyar ADP na ƙasa da na jihar Kano har ma da ɗan takarar gwamnan jihar Jigawa a jam’iyyar.

Slide Up
x