Hukumar Alhazai ta sanar da kuɗin da maniyyata za su fara biya don aikin Hajjin badi a Kano

Danpaffa

Hukumar Jin Dadi da Walwalar Alhazai ta jihar Kano ta sanar da Naira Miliyan 8.4 a matsayin wani ɓangare na kuɗin aikin Hajjin baɗi da kowanne maniyyaci zai ajiye.

Alfijir labarai ta rawaito shugaban hukumar, Alhaji Laminu Rabi’u Danbappa ne ya baiyana hakan yayin wat ganawa da jami’an aikin Hajji na kananan hukumomi a shelkwatar hukumar.

A wata sanarwa da kakakin hukumar, Suleman Dederi ya fitar a jiya Litinin Kano, Danbappa ya ce Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON ce ta bada umarnin a sanar da Naira Miliyan 8.4 a matsayin kason farko na kuɗin aikin Hajjin 2025.

Ya kuma hori maniyyatan da su tabbatar sun biya kudaden su a kan lokaci.

Hakazalika Danbappa ya sanar da cewa NAHCON ta baiwa Kano kason kujerar alhazai 4,356, wanda a cewar sa, za a rarraba su a kananan hukumomi 44 na jihar.

Ya kuma sanar da cewa jihar Kano ta fara shirye-shiryen aikin Hajjin na baɗi, inda ya yi fatan a yi shi cikin nasara.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *