Hukumar INEC Ta Sanya Ranar Gudanar Da Zaben Gwamna A Jihohi Uku

Alfijr ta rawaito za a gudanar da zaben gwamnonin jihohin Imo, Bayelsa da Kogi a ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023, kamar yadda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana.

Alfijr Labarai

Hukumar ta bayyana hakan ne a taronta na mako-mako da ta saba gudanarwa a ranar Talata.

kwamishinan INEC na kasa kuma shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu zabe, Festus Okoye ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya sanyawa hannu a ranar Talata.

Okoye ya ce an shirya gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyun siyasa a jihohin ne daga ranar 27 ga Maris zuwa 17 ga Afrilu, 2023.

Ya kuma bayyana cewa matakin ya cika sharuddan sashe na 28 (1) na dokar zabe ta 2022, wanda ya wajabta wa INEC da ta wallafa sanarwar zaben, kwanaki 360 kafin ranar da za’a gudanar da zaben.

Alfijr Labarai

Hazalika wa’adin gwamnan jihar Imo mai ci zai kare ne a ranar 14 ga watan Janairun 2024 yayin da na jihohin Kogi da Bayelsa zai kare a ranar 26 ga watan Janairun 2024 da 13 ga Fabrairu 2024 ko wannen su. In Ji shi

INEC ta kuma kara da cewa za a wallafa sanarwar zaben gwamna a jihohi uku a ranar 14 ga Nuwamban shekarar 2022.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *