Hukumar Kashe Gobara Ta Kano Ta Ceci Rayuka 72, Da Dukiya Ta 38,600,050.00


Alfijr ta rawaito Hukumar Kashe Gobara Ta Jihar Kano Karkashin Jagorancin Darakta Alh. Hassan Ahmad Muhammad ta bayyana cewar a watan Satumba 2022, hukumar kashe gobara ta jiha ta samu kiran gaggawa daga gidajen kashe gobara 27dake fadin jihar

Alfijr Labarai

Bayanin hakan na kunshe cikin wata sanarwa da kakakin rundunar Saminu Yusuf ya fitar a yau talata, in da ya bayyana cewar, cikin watan da ya gabata mun samu kiran kashe gobara, dai karya, adadin kiran ya kasance kamar haka.

*Mun sami kiran kashe wuta guda sha bakwai 17.

*Mun sami kiran ceto 49.

*Adadin Kiraye kirayen karya da muka samu 11

* Kiyasin kadarori da gobarar ta lalata: 14,850,000.00k

* Kiyasin kadarorin da hukumar suka ceto: 38,600,050.00k

*Jimillar adadin wadanda suka mutu a watan Satumba mutum 9 ne.

Alfijr Labarai

Kakakin hukumar Saminu Yusuf ya kuma bayyana cewar

*Adadin mutanen da muka yi nasarar ceto daga bala’in gobara daban-daban 72.

Ya kara da cewa za mu yi amfani da wannan damar wajen ba jama’a shawarar su kula da wuta don gujewa tashin gobara.

Bugu da ƙari, a kiyaye dokar hanya don guje wa faruwar haɗarin mota.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *