Hukumar Kashe Gobara Ta Kano Ta Tabbatar Da Mutuwar Wani Yaro Sakamakon Faɗawa Rijiya

Alfijr ta rawaito hukumar kashe gobara ta jihar Kano, ta tabbatar da mutuwar wani yaro sakamakon faɗawa rijiya a titin Jajira da ke yankin ƙaramar hukumar Tofa.

Alfijr Labarai

Kakakin hukumar Saminu Yusuf Abdullahi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a ranar Litinin.

Ya ce, a ranar Lahadi 30 ga Oktoba, 2022 ofishin kashe gobara na ya samu kiran kiran gaggawa da misalin karfe 1:05 na rana daga Mahmud Ibrahim wanda ya ba da rahoton faruwar lamarin.

Haka kuma ya ce, “Lokacin da mutanen mu daga babban ofishin kashe gobara suka isa unguwar da misalin karfe 1:23 sun gano cewa, wani yaro ɗan kimanin shekara 17 mai suna Zayyanu Muhd, ne ya fada cikin wani kududdufi inda aka ceto shi cikin mawuyacin hali wanda kuma daga bisani kuma aka tabbatar da mutuwarsa.”

Bayan haka kuma an mika gawarsa ga Baturen ƴan sanda na Bachirawa Uba Shehu.

Alfijr Labarai

Haka kuma, Hukumar ta bayyana cewar tana nan tana bincike kan dalilin faruwar lamarin.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *