Hukumar tace fina-finai ta haramta gudanar da bikin ‘Ƙauyawa Day’ a Kano

IMG 20250517 154846

Hukumar tace fina-finai ta Jihar Kano, ta dakatar da dukkanin cibiyoyin gudanar da taro da ke faɗin jihar, tare da haramta gudanar da bikin ‘Ƙauyawa Day’ gaba ɗaya.

Shugaban hukumar, Abba El-Mustapha ne, ya bayyana hakan a ranar Asabar, bayan wata ganawa da masu ruwa da tsaki a jihar.

Ya ce wannan mataki na cikin sabuwar doka da majalisar dokokin Jihar Kano ta amince da ita, kuma Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya sanya wa hannu.

Sabuwar dokar ta bai wa hukumar ikon sanya ido da kula da dukkanin cibiyoyin taro da ayyukan DJ a jihar.

An ɗauki wannan mataki ne bayan ƙorafe-ƙorafe daga wasu ƙungiyoyin addini da na al’adu kan yadda ake gudanar da bikin Ƙauyawa Day.

Galibin waɗannan bukukuwa matasa da ƴan mata ne ke shirya su, amma ana zargin suna haifar ɗabi’un da ba su dace ba.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan  👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *