Wata tanka ɗauke da man fetur ta yi sanadiyyar kashe kusan mutum da 100 a jihar bayan ta fashe tare da kamawa da wuta.
Alfijir labarai ta rawaito Kakakin rundunar ƴansandan jihar, DSP Lawan Shiisu Adam, ya tabbatar da mutuwar mutum 94 zuwa lokacin hada wannan rahoton.
Ya ƙara da cewa hatsarin da ya faru ranar Talata da tsakar dare, kuma ya raunata wasu mutanen kusan 50.
Babbar jami’ar hukumar kiyaye haɗurra a Jigawa, Aishatu Sa’adu, ta shaida wa BBC cewa Ibtila’in ya faru ne a garin Majia da ke ƙaramar hukumar Taura bayan da direban tankar ya kauce wa wata babbar mota ɗauke da tumatur.
Hakan ya sa direban tankar ya faɗa gefen titin har kan motar ya rabu da gangar jikinta, lamarin da ya sa fetur ɗin da yake dako ya malale titi da kwatoci a gefen hanyar.
DSP Lawan ya ce ganin haka ne ya sa mutane suka yi dafifi a wurin da lamarin ya faru domin kwasar man da ya zuba a ƙasa bayan sun ci ƙarfin jami’an tsaron da ke korarsu a ƙokarin kauce wa tashin gobara.
Shaidu sun shaida wa BBC cewa tankar ta yi kusan awa biyu tana ci da wuta kafin jami’an kashe gobara su yi nasarar kashe ta.
Zuwa yanzu ana shirin yin jana’izar mutanen da suka mutu sakamakon fashewar tankar.
Hotunan da aka turo wa Alfijir labarai sun nuna yadda aka lulluɓe gawarwakin mutanen da ganyayyaki, yayin da wasu hotunan suke ɗauke da gawarwakin da suka rasa wasu sassa na jikinsu.
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj