Rushewar gini yayi sanadiyar mutuwar uwa da ƴaƴanta uku a karamar hukumar Zaria da ke jihar Kaduna.
Alfijir labarai ta rawaito marigayiya Malama Habiba Nuhu ta rasu ne tare da ‘ya’yanta biyu da jikarta ɗaya an unguwar Karauta da ke cikin garin na Zariya.
Wani ɗan uwa ga iyalan da suka rasu, Malam Ahmad Ibrahim, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 3:30 zuwa 4:00 na daren ranar Laraba a lokacin da bangon makwabcinsu ya faɗa kan ɗakinsu, lamarin da ya sa aka gaggauta kai mijin marigayiyar Malam Nuhu Dogara zuwa asibiti domin samun agajin gaggawa.
Allah ya jikansu da Rahma ! Allah ya bamu damina mai albarka ameen.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t