Majalisa Ta Gargadi Ga Masu Binciken Kudi Na Kananan hukumomi

B6

Majalisar Dokokin jahar kano ta gargadi masu binciken kudi na kananan hukumomi akan su rika adana bayanan kashe kudade bisa tanadin doka.

Alfijir labarai ta ruwaito garadin na kunshe a cikin rahoton kashe kudaden kananan hukumomi na shekarar 2019 da kwamitin Kula da kashe kudaden gwamnati na Majalisar ya gabatar dangane da rahoton binciken kashe kudaden kananan hukumomi da babban mai binciken kudi na kananan hukumomin ya aikewa Majalisar.

A yayin da yake gabatar da rahoton, Shugaban kwamitin kuma Dan Majalisa mai wakiltar karamar Hukumar Fagge Alh. Tukur Mohd ya bukaci ma’aikatar kananan hukumomi ta dauki matakan  canza tsarin kididdiga da adana bayanai daga tsohon tsari zuwa Sabo. 

Kazalika Majalisar ta bukaci Ma’aikatar kudi ta sa mai binciken kudi ya rika buga bayanan kashe kudade daga asusun kananan hukumomi duk shekara domin adana bayanansu na shekara.

Zaman Majalisar wanda Shugaban Majalisar Alh. Jibril Ismail Falgore ya jagoranta ya ja hankalin shugabanin kananan hukumomi su fadada hanyanyin samun kudaden shigar su dana kadarorinsu musamman hannun jari da kasuwanni da tashoshin mota da kasuwannin dabbobi da mayanka tare inganta su domin samun kudaden shiga yanda yakamata a madadin dogara da kason gwamnatin tarayya.

A yayin da take amincewa da rahoton kwamitin, Majalisar ta ce za ta kafa kwamitin da zai  bibiyi inda kudaden kananan hukumomi suka makale domin mayar da su tare da daukar matakan hana diban kudin gwamnati da nufin saka su a wani gurbi.

Rk

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *