Innalillahi wa Inna Ilaihirraji’un! Allah ya yiwa Sheikh Jingir Rasuwa

FB IMG 1741270812005

Ƙungiyar Jama’atu Izatil Bidi’ah Wa Ikamatus Sunnah ta rasa ɗaya daga cikin manyan malamanta, Sheikh Hassan Saeed Jingir, wanda ya rasu yau sakamakon rashin lafiya.

Sheikh Jingir na daga cikin manyan malaman ƙungiyar da suka kwashe shekaru sama da 40 suna karantarwa a matakai daban daban, cikin su harda Babbar Kwalejin Ƙaratun addinin Islama dake Jos, wato SHIS.

Marigayin ya rike muƙamai daban daban, cikin su harda shugaban Majalisar Izala na Jihar Filato da kuma mataimakin shugaban ƙungiyar Izala na ƙasa baki ɗaya.

Bayan darewar Izala gida biyu, an yi sulhu tsakanin bangarorin biyu, abinda ya kai ga saukar Sheikh Saeed Jingir daga muƙamain mataimakin shugaba na ƙasa, domin bai wa Sheikh Yusuf Sambo Rigachikum kujerar, yayin da Sheikh Sani Yahya Jingir ya ci gaba da rike shugabancin ƙungiyar baki daya.

Wannan ya sa aka bai wa marigayin mukamin Sa’i na ƙasa kuma ɗaya daga cikin ƴan majalisar gudanarwar ƙungiyar Izala ta ƙasa baki daya.

Tuni malamai daga sassa daban daban na ciki da wajen Najeriya suka fara aikewa da saƙon ta’aziyar rasuwar shehun malamin.

Cikin waɗanda suka aike da saƙon ta’aziya harda shugaban gwamnonin Arewacin Najeriya kuma Gwamnan Jihar Gombe, Ahaji Inuwa Yahya, wanda ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga al’ummar Musulmi da kuma Najeriya baki ɗaya.

Yahya ya ce Najeriya ta yi rashin gudumawar da malamin ke bayarwa wajen ilmantarwa da da faɗakarwa da kuma kira wajen haɗin kan jama’a.

Yanzu haka an gudanar da sallar jana’izarsa a Masallachin Juma’ar Unguwar Rimi dake birnin Jos. Allah ya jikansa da gafara Ameen Ameen.

RFI

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *