Innalillahi wa Inna Ilaihirraji’un! Sabon mai baiwa Gwamnan Kano shawara ya rasu kwana ɗaya da rantsar da shi

FB IMG 1736344141585

Sabon mai baiwa Gwamnan Kano shawara kan aiyuka, Injiniya Ahmad Ishaq Bunkure ya rasu, kwana ɗaya da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya rantsar da shi a gidan gwamnati.

A wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya fitar, marigayin ya rasu a yau Laraba a kasar Egypt.

Ya ce Gwamna Yusuf, wanda ya nuna kaɗuwa ga rasuwar Bunkure, ya baiyana mutuwar ta sa matsayin babban rashi ga iyalinsa da ma Kano baki ɗaya.

“Wannan wani yanayi ne na kaɗuwa da alhini saboda Injiniya Bunkure mutum ne mai hazaƙa da sanin makamar aiki wanda jihar Kano za ta amfani da shi.

” Allah Ya gafarta masa Ya baiwa iyalin sa da mu baki ɗaya hakurin rashin sa,” in ji Gwamnan.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *