Iran ta yi gargaɗin kawar da  shugaban Amurka Danald Trump daga duniya

FB IMG 1773071589553

Wani babban jami’in tsaron Iran, Ali Larijani, ya yi gargaɗi ga shugaban Amurka Donald Trump, inda ya ce ya kamata ya yi hankali domin kada a “kawar da shi daga duniya”.

A wani saƙo da ya wallafa a shafin X, Larijani ya ce Iran ba ta jin tsoron abin da ya kira “barazanar Trump mara amfani.”

Ya ce, “Ko waɗanda suka fi ka ƙarfi ba su iya kawar da al’ummar Iran ba.”

Sai ya ƙara da cewa, “Ka yi hankali, kada a kai ga kawar da kai daga duniya.”

Wannan furuci na Larijani ya zo ne bayan Trump ya yi barazana a dandalinsa na Truth Social cewa Amurka za ta zafafa hare-harenta kan Iran idan ba ta buɗe mashigar Hormuz ba wadda ke da muhimmanci wajen safarar man fetur a duniya.

BBC

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *