Daga Aminu Bala Madobi
Wasu fusatattun matasa a yankin Otor-Owhe da ke karamar hukumar Isoko ta Arewa a jihar Delta, sun kone wani mutum bisa zargin fille kan wata mata.
Rahotonni sun bayyana cewa marigayin mai suna Oghenero ya fille kan matar ne a daji bayan ta mari mahaifiyarsa.
Wani ganau da ya zanta da wakilin Sahara Reporters ya ce, “Matar da aka fillewa kan ta ‘yar asalin Emevor ne da Orogun ta mari mahaifiyar mutumin ne bisa wata takaddama.
Lokacin da ta isa gida, mahaifiyar wanda ake zargi da fille kan matar ta sanar da shi abin da ya faru tsakaninta da matar da ta rasu.
“Nan da nan sai Oghenero ya fita dajin a fusace kai tsaye ya nufi inda take, ya tarar da matar tana noma baiyi wata-wata-ba ya sare mata kai ya dawo gida.
“Da ya isa gida, ‘yan banga na yankin suka kame Oghenero kuma suka harbe shi a kafafu yayin da yake kokarin tserewa kafin wasu fusatattun matasan unguwar suka kona shi.”
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Delta SP Bright Edafe, da aka tuntube shi bai amsa kira ko sakon da aka aike ta wayar salula ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.