Jamhuriyyar Nijar ta haramta amfani da babura masu ƙafa uku

FB IMG 1768639928904

Tarar Jaka Hamsin zuwa Ɗari na CFA ne za ta hau kan duk wanda aka samu da laifin bijirewa dokar hana amfani da baburan masu ƙafa Uku

Mahukunta a Jamhuriyar Nijar sun haramta amfani da babura masu ƙafa Uku a birnin Yamai, domin kawo ƙarshen tuƙin ganganci da masu baburan ke yawaita yi, sai kuma karya doka ta hanyar tuƙa baburan masu ƙafa uku ba tare da takardu ba.

Cikin sanarwar da ya fitar, Magajin Garin Birnin Yamai ya ce tarar Jaka Hamsin zuwa Ɗari na CFA ne za ta hau kan duk wanda aka samu da laifin bijirewa dokar hana amfani da baburan masu ƙafa Uku, baya ga tarar kuma a ƙwace abin hawan.

Sai dai a yayin da mahukunta ke cewa sun ɗauki wannan mataki domin bai wa jama’a kariya, wasu na ganin hakan a matsayin matsi a gare su, la’akari da cewa baburan masu ƙafa uku na sama wa marasa ƙarfi sauƙi matuƙa.

RFI HAUSA

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *