Jami an tsaro Sun Shirya Cafke Bashir Gentile Mai Fashin Baki Akan Siyasa A Kano

Alfijr

Alfijr ta rawaito ‘yan sandan Kano na shirin kama wani shahararren mai sharhi kan al’amuran siyasa, Bashir Gentile, kan fadawa gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje gaskiya, a cikin shirye-shiryen gidan rediyon jihar

Alh Bashir Gentile, na hannun damar tsohon gwamnan jihar Malam Ibrahim Shekarau, kuma mai taimaka wa shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ne, yayi fice wajen tsage gaskiya duk dacinta musamman ga gwamnatin jihar kano

Daily Nigerian ta wallafa cewar a baya-bayan nan dai da dama daga cikin masu sukar gwamnan sun fuskanci cin zarafi, tursasawar ‘yan sanda da kuma gurfanar da su a gaban wasu alkalan jihar.

Alfijr

Majiyoyi sun ce bayan yunkurin kama Gentile ya ci tura, a yanzu ‘yan sandan sun gayyace shi domin amsa tambayoyi kan karar da aka shigar da shi, a lokacin da aka tuntubi kakakin rundunar Yan sandan Kano Abdullahi Kiyawa, ya ce bai da masaniya kan gayyatar ko kuma shirin kama shi.

Alfijr ta tuntubi Alh Bashir Jantile kan maganar gayyatar, ya ce kwarai an gayyaci shi, kan karar da gwamnatin Kano tayi akansa ta hannun wani Jami in tattara haraji, amma da yake baya gari ya sanar musu ha da hakan.

Slide Up
x