Hukumar Hisbah Ta Kame Mutane 98, Maza 44 Da Mata 54 Suna Tsaka Da Badala

Alfijr

Alfijr ta rawaito rundunar Hisbah, ta kama mutane 99 a karamar hukumar Kazaure da kuma Dutse jahar Jigawa, suna tsaka da aikata alfasha

Kwamandan rundunar, Malam Ibrahim Dahiru ya tabbatar da aukuwar lamarin a Dutse ranar Talata, 17 ga watan Maris na shekarar 2022

Rundunar ta bayyana cewa cikin wadanda aka kama akwai maza 44 da mata 54, kuma an yi ram da su yayin da suke tsaka da lalata da sauran ayyukan masha’a, rundunar ta kama su a samamen da suka kai daban-daban.

Ya bayyana yadda aka kama mutane 91 cikin masu laifin, wanda cikin su mata 49 da maza 42 a ranar 16 ga watan Maris yayin da suka kai samame kauyen Gada da ke Kazaure.

A cewarsa, ana zargin wadanda aka kama da yin badala tare da yin sauran ayyukan masha’a, sai dai Dahiru ya ce ba a kama 21 daga cikin mazan tare da mata ba.

Alfijr

Kwamandan ya ce an kama sauran mutane 8 din da ake zargi, ciki akwai mata 5 da maza 3 a ranar 17 ga watan Maris a garin Dutse, sun kwace kwalabe 8 na giya yayin da suka kai samamen. Inji shi

Ya ce Hisbah za ta cigaba da kai samame duk wani lungu da sakon da aka san ana aiwatar da miyagun al’amura a fadin jihar.

Alfijr

Dahiru ya kara da yaba wa ‘yan sanda da mazauna yankin akan kokarin su na bayar da goyon baya da kuma hadin kai ga rundunar wanda hakan ya taimaka mata wurin yin ayyukan ta da kyau.

Kamar yadda Legit.ng suka wallafa

Slide Up
x