Jami’ar Yusuf Maitama Sule Kano Ta Haramta Ayyukan Kungiyar ASU, A Makarantar Nan Take.

FB IMG 1776781885714

Editan Alfijir Labarai.

Mahukuntan Jami’ar Ilimi Ta Yusuf Maitama Sule Dake Kano sun sanar da haramta ayyukan kungiyar ASUU dake Jami’ar tare da ayyana kungiyar a matsayin haramtacciya a cikin jami’ar.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa ta cikin gida da magatakardar jami’ar, Malam Sani Danladi Abubakar, ya fitar bayan taron majalisar gudanarwar jami’ar karo na biyar da aka gudanar a ranar 16 ga Afrilu, 2026.

A cikin sanarwar mai dauke da kwanan wata 17 ga Afrilu, 2026, majalisar gudanarwar jami’ar ta bayyana cewa an dauki wannan mataki ne domin hana samuwar kungiyoyi masu kama da juna da kuma hana gudanar da harkokin kungiyoyi ba tare da sahalewar jami’ar ba.

Majalisar ta ce kungiyar ASUU ba ta cikin kungiyoyin da jami’ar ta amince da su, sannan kuma ba ta da rijista a matsayin kungiyar kwadago kamar yadda doka ta tanada, lamarin da ya sa ayyukanta suka zama haramtattu a cikin jami’ar.

Jami’ar ta kuma umarci daukacin ma’aikata da su gaggauta daina shiga, tallatawa ko hada kai da duk wata harka da ta shafi kungiyar da aka haramta. Haka kuma ta gargadi duk wanda aka samu da saba wannan umarni cewa zai fuskanci hukunci daidai da dokokin jami’ar da kuma dokokin aikin gwamnati.

Daganan, jami’ar ta umurci kungiyoyin da aka amince da su na wucin gadi kamar COEASU da SSUCOEN da su fara shirye-shiryen hade wa da manyan kungiyoyin kasa da aka amince da su wato ASUU da SSANU.

Masu ruwa da tsaki na jami’ar sun ce wannan mataki zai tabbatar da bin dukkan ka’idojin kasa da suka shafi kungiyoyin ma’aikata a manyan makarantu tare da tabbatar da daidaito da zaman lafiya a cikin jami’ar.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *