Daga Rabiu Usman
….Idan anyi mana muyi Zabe, idan ba’a yi ba muyi zaman mu a Gidajen mu.
Mazauna Kauyen Sabon Garin Alhazawa dake Cikin karamar hukumar Kiru ta jihar kano na kokawa akan mawuyacin halin rayuwa da suke ciki sakamakon rashin kulawa da suke samu daga Gwamnatoci tsawon sama da Shekaru 25.
Sunce, sun dade suna rayuwa ba tare da samun muhimman abubuwan more rayuwa a yankin su ba musamman a bangaren Hanya, Asibiti da kuma rashin Gyaran wata Babbar Gada da Al’umma na Kananan hukumomi Sama da 5 ke wucewa ta kanta.
Shugaban Kungiyar Cigaban Garin Sabon Garin Alhazawa Gabas da Gari Ina Mafita Yushe’u M Muhammad ne ya bayyana hakan yayin ziyarar gani da Ido ga wakilin Arewa radio Rabiu Usman yayi.
Inda yace Mutanen Garin na kokarin kauracewa shiga zabukan shekarar 2027 me zuwa saboda rashin kyawun hanya da Gadar da suke amfani da ita.
Wasu daga Cikin Dattawan mazauna garin da suka haura sama da Shekaru 60 zuwa 70 a yankin sun bayyana hanyar a matsayin me Dadadden tarihi tun zamanin Sir Ahmadu Bello Sardauna.
Mai Unguwar Turakacci Malam Muhammad Kabiru ya tabbatar da rashin faruwar lamarin, inda yabi sawun mutanen garin wajen yin kira ga Mahukunta musamman gwamnatin kano ta kawo musu dauki sakamakon yanayin Damunar bana da take kokarin sauka.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t