Abdullahi Umar GandujeAsalin hoton,OTHERS
Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta kaɗa ƙuri’ar amincewa da salon jagorancin shugabanta, Abdullahi Umar Ganduje.
A taron da jam’iyyar ta kammala yau Laraba a Abuja, masu ruwa da tsaki na jam’iyyar sun yaba da rawar da Ganduje ya taka tun bayan naɗa shi kan muƙamin a watan Agustan 2023.
Hakan na nufin cewa tsohon gwamnan na jihar Kano zai ci gaba da jagorancin jam’iyyar har zuwa lokacin da za a yi babban taronta na ƙasa, inda za a zaɓi cikakken shugaba.
A watan Agustan 2023 ne kwamitin gudanarwa na jam’iyyar ya tabbatar da Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar na riƙo na ƙasa, bayan ajiye aikin shugaban jam’iyyar da ya gabace shi, Sanata Abdullahi Adamu.
BBC
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ