Wata babbar tawaga ta jam’iyyar PDP karkashin jagorancin Tanimu Turaki ta gudanar da ganawar sirri da shugabannin jam’iyyar ADC da David Mark ke jagoranta a birnin Abuja kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta rawaito.
Rahotanni sun ce tawagar ta PDP ta isa gidan Mark da ke Apo Legislative Quarters da misalin karfe 4:50 na yamma a ranar Laraba.
Majiyoyi sun bayyana cewa ganawar na daga cikin tattaunawa da ake yi domin duba yiwuwar kulla kawance tsakanin PDP da ADC gabanin babban zaben shekarar 2027.
Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde; tsohon ministan yada labarai kuma jigo a PDP, Jerry Gana; da tsohon gwamnan jihar Neja, Babangida Aliyu, tare da mambobin kwamitin gudanarwa na jam’iyyar (NWC).
Haka kuma, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar; dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi; tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso; da tsohon gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal, duk sun halarci taron.
Sauran sun hada da tsohon gwamnan Rivers, Rotimi Amaechi, da tsohon Ministan Shari’a na kasa, Abubakar Malami.
Ana sa ran shugabannin jam’iyyun biyu za su yi bayani ga manema labarai bayan kammala ganawar.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t