Daga Aminu Bala Madobi
Jam’iyyar PDP ta kori tsohon Gwamnan Jihar Ribas kuma Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike; sakataren jam’iyyar, Samuel Anyanwu; da kuma tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose, daga jam’iyyar kan zargin ayyukan da suka saba wa jam’iyyar.
Kudirin korar nasu wanda ‘ya’yan jam’iyyar suka amince da shi a ranar Asabar a babban taron jam’iyyar PDP na kasa da ke gudana a birnin Ibadan, wanda daya daga cikin iyayen jam’iyyar Cif Bode George ne ya gabatar da shi, sannan gwamnan jihar Bauchi Bala Mohamed ya goyi bayansa.
Sauran wadanda aka kora sun hada da mai baiwa jam’iyyar shawara kan harkokin shari’a, Adeyemi Ajibade SAN, Umar Bature, AbdulRahman Mohammed, Mao Chuambuwa, George Turner, Austin Nwachukwu, Abraham Ammah dakuma Dan Orbih.
Muna tafe da sauran labaran
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t