Asibitin Best Choice Specialist Ya Mallaki Na’urar Endoscopy Irinta Ta Farko A Kano

Alfijr Labarai

Alfijr ta rawaito Shugaban Asibitin Best Choice Specialist Hospital da ke Kano, a unguwar Sabuwar Gandu Auwal Muhammad Lawal, a ranar Lahadin ya bayyana cewa yanzu haka asibitin ya samu sabuwar na’urar da za a iya amfani da ita, wadda ita ce irinsa ta farko a fadin jihar Kano.

Endoscopy

Alfijr Labarai

Ya ce, sabuwar na’ura ta kudade masu nauyin gaske wadda za ta saukaka aikin tiyata a cikin cututtukan  da suka shafi  mafitsasara  Koda, fibroids, gano matsalar ciwon ciki da ciwon daji wanda wannan wani kari ne a cikin jerin kayan aikin fasaha a asibitin.  Best Choice Specialist.

A cewar Lawal,  asibitin  ba kayan aiki  aka cika  shi da kashi ba  kawaii, akwai  isassun ma’aikata da kwararrun Likitoci don biyan bukatar al umma.

Best Choice a halin yanzu tana da likitocin dindindin guda ashirin (20),  sannan kuma  kwararrun likitocin a kowane fanni dake zuwa a duk lokacin da bukatar hakan ta tashi domin samun ingantacciyar lafiya

Yanzu haka a Best Choice mun kawo wata na’ura wadda itace irin ta farko a jihar kano

Alfijr Labarai

Da wannan na’ura, ayyukanmu za su kara inganta  fiye da baya, kuma yawan masu aiko da sakonnin da muke samu daga ko’ina a fadin jihar saboda ingancin ayyukan da muke bayarwa zai kara karuwa”.

Auwal ya ci gaba da cewa, asibitin da ke Sabuwar Gandu ya fara da dakunan da bai wuce 4 ba amma a yau yana iya alfahari da gadaje 50 ga dakuna na musamman wato (VIP)

Babban burin da muka saka a gaba  a wannan asibitin,shi ne, taiimakawa al-umma duba da irin wahalar da mutane suke sha a fannin lafiya

Asalin asibitin namu clinic ne, daga bisani muka fadada tunaninmu ya koma specialist, wato muna iya tunkarar kowace irin cuta kenan da yardar Allah kuma a samu nasara.

Alfijr Labarai

Dakin Likita

Alhamdulillah a Best Choice yanzu haka muna da likitocin da suka ƙware wajen larurar  mahaifa,  haihuwa, yara,  zuciya, kwakwalwa.

Haka zaliika muna da sashin kulawa na musamman ga jarirai, musamman abin da suka shafi, Urology,  Kunne Hanci  da  makogwaro da sashin kula da kashi kuma duk waɗannan, suna kan farashi mai  rahusa.

Yunkurin da muka yi tsawon shekaru ya yi nisa wajen yaba kokarin gwamnati na samar da ayyukan yi ga matasa a jihar duba da yawan likitocinmu da sauran ma’aikatanmu,” inji shi.

Bugu da kari, ya bayyana cewa asibitin na kokarin a kullum don saduwa da abokan hulda da gamsuwa wanda hakan ya sa a kullum suke neman sabbin na’urorin da za su iya kula da marasa lafiya da su.

Alfijr Labarai

A Best Choice babban burinmu shine mu iya biyan  buƙatun majiyyatan mu shine dalilin da yasa ko yaushe muke yin bincike akan injuna mafi ya kyau.

Ba ma  jinkirin  ko sanya  wajen siyan kowace na’urar da za ta iya taimaka mana a aikinmu kuma ya ba abokan cinikinmu, don  samun gamsuwa  ga  abokanan  huldarmu.”

Shugaban yayi kira ga jama’a da su garzayo asibitin Best Choice Specialist Hospital a duk lokacin da suke buƙatar taimakon likita.

Alfijr Labarai

Don Neman Karin Bayani A Tuntubesu A Wannan Lambobin Ko Ta Yanar Gizo

+2348036073989 +2348038029624

www.bestchoiceclinick.com

Slide Up
x