KAMFANIN AMMASCO Ya Horar da Kanikawa kan Tantance Man Juye da Fasahar CNG a Kano

IMG 153539 21526 1779374155541

Editor

Kamfanin Ammasco Lubricant ya shirya wani horo na musamman ga kanikawa daga sassa daban-daban na kasar nan domin kara musu ilimi kan yadda za su tantance ingancin man juye tare da fahimtar irin man da ya dace da nau’o’in ababen hawa daban-daban. An gudanar da shirin ne a jihar Kano domin inganta fahimtar masu sana’ar gyaran motoci kan tasirin mayukan lubricants.

Da yake jawabi yayin bitar taron manema labarai, Manajan Daraktan kamfanin, Alhaji Ibrahim Mustapha Ado, ya bayyana cewa horon na da nufin koyar da kanikawa dabarun gano bambanci tsakanin man juye mai inganci da mara inganci, musamman duba da yadda sabbin fasahohin motoci ke kara shigowa kasar nan.

A cewarsa, kamfanin ya gayyato kanikawa da masana daga fannoni daban-daban, inda har da wasu abokan hulɗa na fasaha daga ƙasar Ingila domin ilmantar da mahalarta kan yadda ake tafiyar da injinan CNG, masu amfani da fetur da kuma diesel. Ya jaddada cewa kowacce mota tana da irin man juye da ya dace da ita, wanda rashin amfani da wanda ya dace kan iya janyo matsaloli ga injin mota.

Tunda farko dayake jawabi, Manajan Sashen Kasuwanci da Ciniki na Kamfanin Ammasco, Alhaji Abubakar Ayuba Matazu, ya bayyana cewa an shirya taron ne musamman domin wayar da kan kanikawa kan muhimmancin tantance ingancin man kamfanin, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen tabbatar da dorewar injinan ababen hawa da rage matsalolin lalacewa.

Ana sa jawabin, Sakataren Kanikawa na Kasa, Ambassador Musa Yahaya, ya yabawa kamfanin bisa wannan shiri, yana cewa kafin zuwan Ammasco suna fuskantar ƙarancin ilimi kan bambancin mayukan juye, amma yanzu sun fara fahimtar yadda ake anfani da su yadda ya kamata, musamman a wannan lokaci da ake kara anfani da fasahar CNG a kasar nan.

Ya kara da cewa makasudin shirin shi ne tabbatar da cewa kanikawa da direbobin baburan adaidaita sahu sun samu cikakken ilimi kan anfani da bakin mai da kuma sabbin fasahohi.

Kamfanin ya kuma tabbatar da cewa zai ci gaba da shirya makamantan bitoci domin samar da ingantattun kayayyaki tare da binciko sabbin fasahohin da za su taimaka wajen inganta ababen hawa.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *