Dubun alƙalin bogin ta cika ne bayan da ya gabatar da kansa a matsayin alkali daga Jihar Jigawa a gaban Kotun Musulunci da ke unguwar Kurna, Ƙaramar Hukumar Fagge.
Alfijir Labarai ta rawaito dubun alƙalin bogin ya tonu ne a lokacin da ya je kotun neman belin wasu mutane biyu wadanda ake zargi da laifin damfara da cin amana.
Kotun ta amince da ba shi belin mutanen ne a bisa sharaɗin sai ya kai jami’an kotu gidansa, amma nan take ya ƙi amincewa.
Da aka tsananta bincike daga baya sai aka gano cewa ungulu da kan zabi ya yi, ma’aikacin shari’a ne, amma bai taɓa zama alkali ba.
A lokacin da aka gurfanar da shi, ya amsa laifinsa, sannan ya roki alkali ya yi masa sassauci.
Khadi Umar Lawan Abubakar ya ba da umarnin tsare shi a gidan yari zuwa ranar 23 ga watan Satumba, 2024 domin ci gaba da shari’ar.
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj