Kasar Saudiyya Ta Magantu Kan Harin Ta’addancin Da Aka Kai Wa Al’ummar Yobe

Yarima

Ofishin jakadancin Saudiyya a Nijeriya ya yi Allah-wadai da harin ta’addancin da aka kai kan al’ummar Mafa da ke karamar hukumar Tarmuwa a jihar Yobe.

Alfijir Labarai ta rawaito cewa, wasu ‘yan ta’addan da ake zargin ‘yan Boko Haram ne sun afkawa al’umma a ranar Lahadin da ta gabata, inda suka kaddamar da ta’addancin da ya kai ga kashe dimbin mazauna garin Mafa.

Shaidun gani da ido sun ce, maharan sun afkawa kauyen ne a kan babura da tsakar daren Lahadi, inda suka yi ta harbe-harbe kan mai uwa da wabi, hakan ya yi sanadin mutuwar  mazauna kauyen ciki har da kananan yara da tsofaffi.

Sanarwar wacce ta fito daga ofishin Jakadancin kasar, ta jaddada yadda Masarautar Saudiyya ke adawa da duk wani nau’in tashe-tashen hankula, ta’addanci, da tsattsauran ra’ayi, tare da jaddada aniyarta na tabbatar da zaman lafiya da tsaro a duniya.

Sannan ta mika sakon ta’aziyyar Masarautar tare da jajantawa iyalan wadanda lamarin ya shafa, gwamnatin Nijeriya da al’ummar jihar Yobe.

Leadership

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *