Kifi Na Ganinka: Nan da makonni uku zan hakura da yaƙi da Iran – In Ji Trump

FB IMG 1773071589553

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Amurka zata fice daga yaƙin da take yi a Iran nan da makonni biyu zuwa uku masu zuwa ko an cimma yarjejeniya ko akasin haka.

Wannan na zuwa ne ƙasa da sa’o’i 48 bayan da yayi barazanar kassara tattalin arzikin Iran ta hanyar ƙwace iko da tsuburin Khargh, fasa cibiyoyi lantarki da kuma lalata na’urorin tacewa da kuma rarraba ruwan sha a ƙasar.

Yayin da yake tattaunawa da manema labarai a ofishin sa da ke fadar White House, Trump ya shaida cewa nan ba da jimawa Amurka zata fice daga Iran ko da yarjejeniya ko babu.

Wannan shine karon farko da Trump ya bayyanawa duniya wani sahihin lokaci na dakatar da yaƙin, wanda a yanzu ya zarce wata guda ana gwabza shi.

Wasu na ganin wannan mataki na Trump baya rasa nasaba da mastin lambar da yake samu daga cikin gida game da yadda ya rungumi yaƙin da bashi da wani amfani ga Amurka illa haddasa mata asarar biliyoyin daloli da kuma jefa rayukan sojojinta cikin haɗari.

Ko da yake amsa tambaya kan hanyoyin da za’a bi wajen kawo ƙarshen yaƙin, sai Trump ya ce ba dole sai Iran ta shiga yarejejeniya ko kuwa an cimma wata jituwa mai ma’ana ba, a’a lokaci dai ya yi da ya kamata Amurka ta janye ne.

Sai dai wani abu da ya ɗauki hankali game da waɗannan kalamai na Trump shine, yadda ya ce kafin cikar makonnin uku, Amurka zata tabbatar da cewa Iran bata sake samun wata damar ci gaba da ƙera makamin Nukiliya ba.

RFI Hausa

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *