Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa tsohon Ministan Lantarki Saleh Mamman hukuncin ɗaurin shekaru 75 a gidan yari.
A ranar Larabar nan ce Babbar Kotun Tarayya ta yanke masa hukunci bayan samun Saleh Mamman da laifin almundahanar Naira biliyan 33 da ɗoriya a lokacin da yake ministan.
Kuɗaɗen da aka gurfanar da shi kansu sun haɗa da na aikin tashar samar da wutar lantarki ta Mambilla da ke mahaifarsa Jihar Taraba, da kuma Tashar Samar da Wutar Lantarki ta Zungeru a Jihar Najeriya.
Kotun ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekara 75 a kurkuku ne bayan tabbatar da duk laifuka 12 da ake tuhumar sa da aikatawa.
Cikakken bayani na nan tafe…
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t