Kotu Ta Aike Da Tsohohuwar Minista , Sarah Ochekpe Da Wasu Mutane Biyu Gidan Yari Na Shekaru Shida

Alfijr

Badakalar Diezani Na Cin Hanci Na N450m: Tsohohuwar Minista , Sarah Ochekpe da wasu mutane biyu za su yi zaman gidan Yari na shekaru shida

Alfijr

Alfijr ta rawaito mai shari’a H.M.Kurya na babbar kotun tarayya dake zama a Jos, Jihar Plateau, ranar Talata 22 ga watan Fabarairu ya yankewa tsohuwar minister albarkatun ruwa karkashin gwamnatin tsohon shugaban Kasa Goodluck Jonathan, Sarah Ochekpe da wasu mutane biyu. Evan Leo Sunday Jitong da Raymond Dabo mataimakin daraktan kamfe na Goodluck/ Sambo 2015, da tsohon chugaban riko na jam’iyyar PDP a Plateau hukuncin zama gidan gyaara halinka na shekaru shida.

Hukumar EFCC ce ta gurfanar da su a gaban mai shari’ar akan tuhuma uku masu alaka da hadin baki da karkatar da kudin haram.

Alfijr

EFCC na zargin su da karban cin hanci na na kudi har kimanin miliyan dari hudu da hamsin daga bankin Fidelity in da wasu kamfanonin mai da tsohuwar minister mai Diezani Alison- Madueke don canza sakamakon zabe na 2015.

Duk da sun bayyana cewa sun mika kudin ga tsohon sanata, marigayi Gyan Pwajok dan takara gwamna karkashin jam’iyyar PDP a 2105, sun gaza kawo wasu shaidu akan haka.

Alfijr

Kotu ta kama su da laifi inda ta yanke musu hukunci akan tuhuma ta farko mai alaka da hadin baki wajen karban kudin da ya wurin dokar hana safarar kudin haram, inda aka yanke musu hukuncin shekaru uku ko su biya tarar N2,000,000.00 (Naira Miliyan Biyu) kowannensu.

Haka kuma kotu ta yanke musu hukuncin shekaru uku akan tuhuma ta biyu ko su biya tarar N2, 000,000 N2,000,000.00 (Naira Miliyan Biyu) kowannensu

Alfijr


Sai dai kuma kotu ta wanke su akan tuhuma ta uku.