Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta aika sammaci ga Gwamnan Babban Bankin Ƙasa, Olayemi Cardoso da ya bayyana a gabanta game da shari’ar da ake yiwa kamfanin crypto na Binance.
Alfijir Labarai ta rawaito cewa kotun ta ce Cardoso zai bayyana gabanta da wasu takardun bayanai a a ranar 2 ga watan Satumba.
Duk da cewa, mai shari’a Emeka Nwite ya dage zaman kotun zuwa 11 ga watan Oktoba, lauyan wadanda ake kara ya bukaci kotun ta sake sanya ranar zaman.
A watan Afrilu ne dai, hukumar EFCC ta gurfanar da shugaban kamfanin Binance, Tigran Gambaryan kan zargin badakalar kudi.
Haka kuma, hukumar tattara haraji ta kasa tana tuhumar Binance da laifin kaucewa biyan haraji.Kotun dai ta bukaci Gwamnan CBN ya bayyana gabanta ko ya tura wakilci.
Haka kuma, kotun ta mika sammaci ga shugaban sashin shari’a na CBN.
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj