Kotun daukaka kara ta amince da saka ranar sake duba hukuncin rataya da aka yiwa makashin Hanifa

FB IMG 1759867271339

Kotun Daukaka Kara dake zamanta a Sakatariyar Audu Bako, Kano, ta bayyana cewa za ta sanar da ranar da za ta yanke hukunci kan neman soke hukuncin kisa da aka yankewa Abdulmalik Tanko da Hashim Isiyaku.

Masu ƙara sun roƙi kotun da ta soke hukuncin kisa da Babbar Kotun Jihar Kano ta yanke musu ta hanyar rataya, tare da sallamar su daga tuhumar.

Lauyan masu ƙara, Barista Attorney Eze Wike, ya nemi kotun da ta rushe hukuncin ƙasa gaba ɗaya tare da sallamar waɗanda ake ƙara.

Sai dai lauyan gwamnatin Jihar Kano, waɗanda ake ƙara, Barista Lamido Abba Sorondinki, yayi suka ga wannan buƙata, inda ya roƙi kotun da ta tabbatar da hukuncin kisa da Babbar Kotun Kano ta yanke.

Alkalan kotun uku da suka saurari ƙarar – Justice Moses Ugo, Justice O. O. Goodluck, da Justice A. R. Mohammed – kuma sun bayyana cewa zasu sanar da ranar yanke hukunci a nan gaba.

Tun a shekarar 2022 Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba 5  ta yanke musu hukuncin kisa bayan ta same su da laifi.

Freedom Radio

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *