Kotun kolin kasar Saudiyya ta Bukaci Al’ummar Musulmi Da Su Duba Jinjirin Watan Shawwal A Ranar Asabar

Alfijr ta rawaito kotun kolin kasar Saudiyya ta bukaci al’ummar musulmin kasar da su duba jinjirin watan Shawwal a daren Asabar 29 ga watan Ramadan shekara ta 1443 bayan hijira,kamar yadda kalandar Umm Al-Qura ta bayyana. Afrilu 30, 2022 AD.

Kotun kolin ta ce duk wanda zai iya ganin jinjirin watan Shawwal da ido ko kuma ta hanyar duban gani da na urar ido to ya kai kara kotu mafi kusa sannan kuma ya yi rajistar shaidarsa.

Wani abin lura shi ne ministan kula da harkokin addinin musulunci, yayi kira da jagoranci Sheikh Dr. Abdullatif Bin Abdulaziz Al-Sheikh ya umurci rassan ma’aikatar da su shirya dukkan masallatai da wuraren ibada na waje domin karbar masallata domin gudanar da sallar Idi.

Alfijr

Al-Sheikh ya sanya lokacin sallar Eid Al-Fitr na shekara ta 1443-2022, wanda zai kasance mintuna 15 bayan fitowar rana kamar yadda kalandar Umm Al-Qura ta tanada.

Slide Up
x