Kotun Minna Ta Yanke Hukuncin Kisa Ta Rataya Kan Wasu Mata 2

IMG 20250118 113732

Daga Khadija Ibrahim Bauchi

Kotun koli ta Minna a Jihar Neja ta yanke hukuncin kisa ta rataya kan wata mata, Amina Aliyu da ‘yar uwarta, Aishat Mohammed, bisa zargin kashe kishiyar Amina, Hafsat Aliyu, da mugunta.

Zainab, ‘yar uwarsu wacce Ć™arancin shekarunta yasa akai mata ta hukuncin É—aurin rai da rai saboda  lokacin da aka aikata laifin shekarunta basu kai ba.

Lamarin ya faru ne a watan Maris na shekarar 2021 a gidan iyali da ke Barkin Saleh, Minna, Jihar Neja.
Amina da Aishat an same su da laifin kashe Hafsat, wadda ita ce kishiyar Amina kuma matar Alhaji Muhammad Sani.

A cewar masu gabatar da ƙara, Aishat ta kai wa Hafsat hari a dakin girki kafin ta cinna wa gawarta wuta.

An fara shari’ar a Kotun Majistare ta Minna mai Lamba Daya kafin a mayar da ita Kotun koli.

A yayin shari’ar an É—auki tsawon shekaru uku ana gabatar da ita, hakazalika shaidu hudu sun bayar da shaida, ciki har da Sani, wanda ya bada labarin yadda Amina ta kashe Hafsat.

Alkalin Kotun koli ta Minna, Mai Shari’a Balkisu Gambo Yusuf, ta tabbatar da cewa masu gabatar da Ć™ara sun tabbatar da Ć™arar su ba tare da wata shakka ba, ta Ć™ara da cewa, “Hukunci ga wanda ya aikata kisan kai a karkashin Sashe 221 na kundin laifukan ya zama kisa ta rataya.”

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *