Daga Aminu Bala Madobi
Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kano ta Aike da Ramlat jarumar TikTok zuwa gidan yari kan zargin badala da karuwanci.
Alfijir labarai ta rawaito a daren Juma’a ne Mai Shari’a Sani Tanimu Hausawa na kotun Musuluncin da ke unguwar Sharada ya sa a ajiye Ramlat a gidan gyaran Hali bayan Hukumar Hisbah ta gurfanar da ita.
A kwanakin nan ne wani bidiyon Ramlat ta ya karade soshiyal midiya, wanda a ciki take tallata madigo, har ta bayyana kanta a matsayin mai wannan dabi’ar.
A cikin bidiyon, an ji matashiyar na cewa, duk wanda zai aureta dole sai ya amince cewa ita za ta auro tata matar, lamarin da ya jawo ce-ce kuce
A kunshin karar laifukan da ake zargin ta da su laifuka ne da suka saba da sashe na 341 da 275 da 227 na Kundin Pinal Kod.
Wacce ake zargin ta amsa laifukan inda ta nemi afuwar kotu bisa laifukan da ta aikata,sai dai saboda kurewar lokaci kotun ta dage shari’ar zuwa ranar 19 ga Fabrairu don yanke hukunci.
Haka kuma kotun ta yi umarnin tisa keyar Ramla zuwa gidan gyaran hali har zuwa ranar da za a sake dawowa gabanta
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V