“Kufito a Gwabza Yaki Don kwatar Mulki Kamar Rayuwarku Zata kare” – In Ji Amaechi

IMG 20250129 WA0137

Daga Aminu Bala Madobi

Gabanin Zaben 2027 dake karatowa, Tsohon gwamnan Jihar Ribas, Rotimi Amaechi, ya bukaci ‘yan Najeriya da su kare kuri’unsu tare da tabbatar da shugabanci na gaskiya a zaben 2027 mai zuwa.

Ayayin dayake tattaunawa da manema labarai a Abuja,  Amaechi ya jaddada cewa ba a ba da mulki kyauta, sai an fafata, inda ya gargadi ‘yan kasa da kada su zauna shiru yayin da ake gwagwarmayar siyasa.

Ya ambaci zaɓen Malam Ibrahim Shekarau a matsayin gwamnan Jihar Kano a matsayin misali, inda ya bayyana cewa himmar jama’a da taruwa cikin yawan gaske ne suka taimaka wajen nasarar Shekarau.

“Dalili daya tilo da yasa Shekarau ya zama gwamnan Kano shi ne saboda mutane sun fito da yawa.

Dayake kwatanta misali da zaben Ghana, Amaechi ya nuna cewa turjiyar jama’a ita ma ta taka muhimmiyar rawa wajen zaben shugaban kasar.

“Kunata kuka da suka, amma babu wanda zai ba ku mulki kyauta, har da ni kaina. Idan kuna son fasto ko liman ya zama Shugaban ku” Inji Ameachi

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *